🧼🧽🧼🧽🧼🧽🧼🧽🧼🧽🧼🧽🧼🧽🧼🧽🧼🧽🧼
✨ WASU HANYOYIN GYARAN FUSKA✨🧼
⇒ _Za a iya hadin ruwan lemun tsami da na zuma sannan a shafa a fuska ko jiki, domin inganta hasken fata da karfafa fatar jiki da kuma hana fesowar kuraje._
⇒ _Akwai hadin ayaba da kwaiduwar cikin kwai da man zaitun. Idan aka yi wannan hadin, sai a shafa a fuska na tsawon minti ashirin sannan a wanke, shi ma wannan hadin domin gyaran fatar jiki da kuma na fuska ne._
⇒ _Hadin ruwan lemun zaki da ruwan kwai da kuma kurkum na da matukar muhimmanci sosai domin yana taimakawa wajen gyaran fata, musamman ma ga amare._
⇒ _Garin bawon lemu wanda sai an busar sannan a daka a tankade sannan a hada da ‘baking soda’ shi ma yana magance cututtukan fata sosai._
⇒ _Akwai hadin ruwan kwakwa da garin bawon lemun zaki da kuma madara. Wannan irin hadin na sanya fata sulbi sosai._
🧼🧽🧼🧽🧼🧽🧼
Sirrin Rike Miji
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA :
Copyright BY: Sirrin Gyaran Jiki
FACEBOOK GROUP: sirrin Gyaran Jiki
EMAIL: sirringyaran234@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin Gyaran Jiki
WhatsApp: +2347026252355
JOIN US TELEGRAM GROUP:
https://t.me/+I7rLPNBVcbA5NDk0
Comments
Post a Comment